Tawagar kwallon kafa ta Algeria ba ta bai wa Sofiane Feghouli, goron gayyata zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar za ta buga a Gabon a 2017 ba.
Tun farko an yi hasashen cewar kociyan Algeria, George Leekens, zai gayyaci Feghouli mai taka-leda a West Ham United zuwa gasar da za a fara a ranar 14 ga watan Janairu.
Sai dai kuma kociyan ya gayyato 'yan wasan kasar da suke buga tamaula a gasar Premier da suka hada da Riyad Mahrez da Islam Slimandi masu wasa a Leicester City da kuma Adlene Guedioura na Watford.
Algeria wadda take rukuni na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, za ka kara da Tunisia da Senela da kuma Zimbabwe.