Back to the West Bromwich Albion Newsfeed

Watakila Sakho ya dawo wasa a kakar bana

Watakila dan kwallon West Ham United, Diafra Sakho ya dawo buga wa kungiyar wasanni a bana, bayan da ya yi jinyar raunin da ya yi a bayansa tun cikin Nuwamba.

Wasanni biyu kacal Sakho ya buga wa West Ham a kakar shekarar nan, sakamakon ciwon baya da ya yi fama da shi.

Sakho mai shekara 27 ya fara yin atisaye shi kadai, bayan da likitoci suka yi masa aiki.

Jami'in da ke kula da lafiyar 'yan wasan kungiyar Stijn Vandenbrouck ya ce idan dan wasa ya dawo daga jinya, yana bukatar makonni hudu zuwa biyar kafin ya dawo murza-leda cikin 'yan wasa.